in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na shirin tallafawa kasashen Afghanistan da Pakistan da bala'in girgizar kasa ta shafa
2015-10-28 20:26:14 cri
Gwamnatin kasar Sin na shirin kai agajin gaggawa kasashen Afghanistan da Pakistan da bala'in girgizar kasar ya shafa.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai, ya kuma bayyana kudurin kasar ta Sin ta kara taimakawa kasashen da abin ya shafa idan har suna bukatar hakan.

Mr Lu ya kuma bayyana cewa, baya ga tallafin gwamnatin kasar Sin kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin za ta baiwa kungiyoyin Red Crescent da ke wadannan kasashen gudummawar dala dubu 100 kowane.

Tuni dai shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aike da sakon ta'aziya ga takwarorinsa na kasashen Afghanistan da Pakistan dangane da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan bala'i.

A ranar Litinin ne dai wata mummunar girgizar kasa mai karfin maki 7.5 ta afkawa yankin arewacin Afghanistan, inda mutane sama da 300 suka mutu a kasashen biyu baya ga gidaje da gine-gine da dama da suka lalace. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China