Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang, ya kirawo jami'in kula da ofishin jakadancin Amurka a kasar Sin Kaye Lee, domin nuna rashin jin dadi ga Amurka kan batun cinikin makamai tsakanin ta da Taiwan.
Zheng ya bayyana hakan ne jim kadan bayan hukumar gudanarwar Amurkan ta sanar da kulla yarjejeniyar cinikin makamai na dala biliyan 1.83 tsakanin ta da Taiwan.
Ya kara da cewa, Taiwan dai wani sashen ne daga yankunan kasar Sin. Kuma kasar Sin ta yi Allah wadai da kulla cinikin makamai tsakanin Amurka da Taiwan.
Zheng ya ce, domin tabbatar da kare martabar kasarta, ya sa kasar Sin ta yanke shawarar daukar dukkannin matakai da suka dace, da suka hada da sanya takunkumi ga kamfanonin dake da ruwa da tsaki a harkar kera makaman da kuma cinikin su.
Zheng ya ce, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta yarjejeniyoyin su uku da suka cimma matsaya kansu, sannan ta soke shirin cinikin makamai da Taiwan, da kuma daina tuntubar sojojin Taiwan, don gudun lalacewar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka kan muhimman tsare tsare.(Ahmad Fagam)