Shugaba Xi Jinping na babban yanki, da Mr. Ma Ying-jeou na yankin Taiwan sun gana ne ranar Asabar a kasar Singapore, a kuma karon farko na haduwar shugabannin sassan tun bayan shekarar 1949. A kuma wannan karo shugabannin sun tattauna da juna cikin kyakkyawan yanayi, tare da musayar managartan shawarwari, da ra'ayoyi, game da alakar dake tsakanin su, inda suka dora muhimmanci kan yadda za su karfafa ci gaban zaman lafiya da bunkasuwa cikin lumana.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa shugabannin biyu, sun yi imani ga irin nasarar da aka cimma a fannin wanzar da zaman lafiya tsakanin sassan tun daga shekarar 2008 kawo wannan lokaci. Daga nan sai suka bayyana burin su na ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar 1992, da karfafa manufar siyasa ta bai daya, tare da wanzuwar ci gaba, da zaman lafiya da kuma tsaro a mashigin tekun Taiwan.
Bugu da kari sassan biyu sun amince su ci gaba da tattaunawa da juna, da musayar ra'ayoyi da zurfafa hadin gwiwa tare da tabbatar da cimma moriyar juna domin amfanin al'ummun su. (Saminu Alhassan)