in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane hudu sun jikkata sakamakon girgizar kasa a Ruwanda
2015-08-08 14:00:03 cri
Hukumar kula da harkokin bala'u da 'yan gudun hijira ta kasar Ruwanda ta bayar da labari a ran 7 ga wata cewa, a wannan rana da sassafe, an yi girgizar kasa a yankin iyakar dake tsakanin kasar Congo-Kinshasa da Ruwanda, wadda ta haddasa jikkatar mutane guda hudu a kasar Ruwanda.

Bisa labarin da aka samu, an ce, cibiyar girgizar kasa din ta fito daga tabkin Tanganyika, kuma yankin da ya fi fama da bala'in yana yankin duwatsu dake lardin Yamma na kasar, wanda yake kusa da tabkin Kivu dake yankin iyakar dake tsakanin kasar Congo-Kinshasa da kasar Ruwanda.

Kana, girgizar kasa din ta riga ta haddasa rasuwar mutane a kalla guda 5 a kasar Congo-Kishasa.

Kuma bisa labarin da shafin intanet na hukumar nazarin yanayin kasa ta kasar Amurka ta bayar, an ce, da safiyar ranar 7 ga wata, an yi girgizar kasa bisa ma'aunin Richter 5.6 a yankin iyakar dake tsakanin kasar Congo-Kinshasa da kasar Ruwanda, kuma asalin aukuwar girgizar kasar din ya kai kilomita 10. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China