A safiyar yau Asabar, kakakin ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, abin da ke jawo hankalin babban yankin kasar Sin shi ne huldar da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, don haka ake fatan matasan sassan biyu za su kara fahimtar juna a mu'amala da hadin gwiwa da ke tsakaninsu.
Kakakin ya fadi haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, inda aka tambaya game da jefa kuri'ar zaben mahukunta a Taiwan, ko mene ne ra'ayin babban yankin kasar Sin a kan sakamakon zaben da za a bayyana?
Kakakin ya ce, tuni mun bayyana cewa, ba za mu tsoma baki ba, abin da muke mai da hankali a kai shi ne huldar da ke tsakanin gabobin biyu.(Lubabatu)