in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in M.D.D. ya yi kira da a warware batun 'yan gudun hijira daga tushe
2016-01-08 11:05:41 cri
Sabon babban jami'in koli na M.D.D.da ke kula da batun 'yan gudun hijira Filippo Grandi, ya bayyana a ranar 7 ga wata cewa, ya kamata a kafa wani tsari, wanda zai taimaka wajen warware batun 'yan gudun hijira daga tushe.

Yayin liyafar da aka shirya a fadar "Nations" dake birnin Geneva, Grandi ya bayyana cewa, batutuwan yaki da talauci manyan hujjoji ne da ke haifar da matsalar 'yan gudun hijira a yanzu. Ya ce akwai bukatar kyautata tsarin da ake aiwatarwa a M.D.D. na yanzu, domin a samu ci gaba da kuma taka muhimmiyar rawar da ta dace.

Yayin da aka tabo batun 'yan gudun hijira na kasashen Turai kuwa, Grandi ya ce, kasashen Turai da dama sun dauki matakai masu yawa na warware batun 'yan gudun hijira, sai dai akwai karancin matakan aiwatarwa.

Ban da wannan kuma, a gabar da ake kokarin tabbatar da tsaron rayuwar jama'a. matakan da za a dauka za su tabbatar da inganta zaman rayuwa, da yadda za su rayu lami lafiya, wanda hakan ya zama babban batu da ya dace a dau matakin warware shi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China