in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan 'yan gudun hijira da suka kaura zuwa nahiyar Turai a wannan shekara ya zarta miliyan guda, inji MDD
2015-12-23 10:51:16 cri

Hukumar kula da al'amurran 'yan gudun hijira da kungiyar kula da al'amurran kaurar jama'a ta MDD, sun yi kididdiga a jiya Talata cewa, ya zuwa ranar 21 ga wannan wata, yawan 'yan gudun hijira da suka kaura zuwa nahiyar Turai ta hanyoyin tekun bahar Rum da sauran kasashe a wannan shekara ya zarce miliyan 1.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa ranar 21 ga wata, yawan makaurata da suka ratsa tekun bahar Rum don tafi nahiyar Turai a wannan shekara ya kai dubu 972.5, kana sauran mutane dubu 34 sun isa kasar Girka da kuma sauran kasashen Turai ta hanyar kasar Turkiyya. Rabin 'yan gudun hijira su ne mutanen kasar Sham da suka rasa gidajensu a sakamakon yake-yake, kana saura kashi 20 cikin dari sun fito daga kasar Afghanistan, kashi 7 cikin dari sun fito daga kasar Iraki.

Domin tinkarar batun 'yan gudun hijirar, wanda shi ne mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu, kungiyar EU ta tsara jerin manufofi, ciki har da raba 'yan gudun hijira zuwa kasashe daban daban na Turai, da kasafta yawan 'yan gudun hijira da kowace kasa ta karba, da kuma habaka cibiyoyin karbar 'yan gudun hijira a yankin Balkan da kasar Girka, amma a halin yanzu, ana gudanar da wadannan manufofi ne a tsanaki (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China