in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin rayuwar 'yan gudun hijirar kasar Sham dake Lebanon na kara tabarbarewa, a cewar rahoton MDD
2015-12-25 11:19:55 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijirar MDD ta fidda wani rahoto a jiya Alhamis a birnin Beirut, wanda ke cewa matsalar 'yan gudun hijira da ake fama da ita, ya gurgunta yanayin rayuwar 'yan gudun hijirar kasar Sham dake kasar Lebanon.

Rahoton ya ce, a sakamakon raguwar taimakon gamayyar kasa da kasa da kuma na kasashen Larabawa, matsalar 'yan gudun hijirar kasar ta Sham ya kara tsananta, kana zaman rayuwar wadanda ke kasar Lebanon ya kara tabarbarewa matuka, wanda hakan ya haifar da babbar barazana ga yanayin siyasa da na tattalin arziki da tsaro a kasar.

Ban da haka kuma, rahoton ya ce kashi 70 cikin dari na 'yan gudun hijirar kasar Shan dake a zaune a Lebanon suna fama da matsanancin talauci, inda kowane mutum bai iya samun dalar Amurka 4 a kowace rana. A daya hannun kuma kashi 2 cikin 3 na yaran suna fama da karancin abinci, kaza lika kashi 50 cikin dari na yaran ne kadai ke iya shiga makarantu, wanda hakan ya tilasa da daman su fara aiki domin daukar nauyin rayuwar su.

Ban da haka kuma, rahoton ya ce, kasashen duniya sun samar da kashi 49 cikin dari ne kacal, na jimillar kudaden da suka yi alkawarin samarwa Lebanon. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China