Sanarwar ta ce, kwamitin ya jaddada wajibcin gurfanar da wadanda suka tsara, aikata da kuma ba da taimako ga wannan laifi a gaban kotu, tare kuma da kalubalantar kasashe daban-daban da su ba da hadin gwiwa ga kasar Saudiyya a wannan fanni bisa dokar kasa da kasa da tanade-tanaden dake cikin kundin tsarin dokokin kwamitin.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Saudiyya ta ba da labari a ran 29 ga wata cewa, an kai harin kunar bakin wake a wani masallaci dake gabashin kasar Saudiyya a tsakiyar wannan rana, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 2, yayin da wasu 7 suka ji rauni.
An ce, tun daga shekarar bara, kungiyar IS mai tsatsauran ra'ayi ta kai hari sau da dama kan wasu masallatai na darikar Shi'a dake gabashin kasar Saudiyya. (Amina)