Hukumomin Riyadh sun bata wa gamayyar kasa da kasa da rai a lokacin da suka bayyana kauracewarsu daga kwamitin tsaro na wa'adin shekaru biyu, kujerar da kasar ta yi takarar nema kuma aka zabe ta a ranar Alhamis a yayin babban taron na MDD.
Shugabannin Saudiyya ya kamata su amince da zamansu a kwamitin tsaro da kuma ci gaba da ba da kokarinsu na bajinta wajen kare bukatunmu, musamman ma a dandalin kwamitin sulhu, in ji gungun wadannan kasashen Larabawa a cikin wata sanarwa.
Wakilan kasashen Larabawa sun bayyana girmamawa da nuna fahimtarsu kan matakin da Saudiya ta dauka dake bayyana matsayin gamayyar kasashen Larabawa da kuma al'ummar musulmi a wannan muhimmin lokaci da tarihi, musamman ma shiyyar yankin Gabas ta Tsakiya, in ji wannan sanarwa.
A ranar Jumma'a ne dai ministan harkokin wajen kasar Saudiyya ya bayyana matakin na kauracewa zama a kwamitin tsaro na MDD har sai an yi wa kwamitin gyaran fasali ta yadda zai cika aikinsa da nauyin dake bisa wuyansa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya. (Maman Ada)