in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yau ne aka fara aikin hajji na shekarar 2014 a kasar Saudiyya
2014-10-03 16:35:28 cri

A yau ne musulmai kimanin miliyan 2 daga kasashe ko yankuna 160 ne suka fara aikin hajji,inda suka taru a filin Arafat.

Hukumar kula da harkokin cikin gidan kasar Saudiyya ta tanadi 'yan sanda da jami'an kashe gobara dubu 85 domin tabbatar da zaman doka da oda yayin aikin hajjin. A sa'i daya kuma hukumar kiwon lafiya ta kasar ta kafa cibiyoyin bincike da sa ido sosai don kula da lafiyar alhazai masu aikin hajji don hana yaduwar duk wata annoba.

An ba da labari cewa, a wannan karo akwai musulmai masu aikin hajji dubu 600 daga cikin kasar ta Saudiyya, yayin da sauran miliyan 1.4 sun zo birnin Makka daga sauran kasashe, akwai kuma musulmai Sinawa dubu 14.5.da ke halartar aikin hajjin na bana. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China