Sarki Salman bIn Abdul-Aziz al Saud ya bayyana hakan ne ta jawabinsa ta kafar yada labaran kasar da suka hada da Talabijin, tare da sanar da zaman makoki bisa ga rasuwar tsohon Sarkin da ya yi Sarauta kusan shekaru 20.
A jawabinsa Sarki Salman ya ambaci halin rudanin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya saboda yaduwar kungiyar mayakan IS, inda yace Larabawa da kasashen Musulmai suna matukar bukatar hadin kai da goyon baya.
Haka kuma, Sarki Salman ya mika ta'aziyar sa ga daukacin al'ummar kasar, da larabawa da ma Musulman duniya baki daya sannan ya jinjina ma Marigayi Sarki Abdallah bisa ga kokarin shi a yankin da sauran kasashen duniya baki daya.
A daga bisani kuma Sarki Salman ya sanar da sabon Yarima mai jiran gado da wassu sabbin mukaman gwamnatin.