in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi a birnin Madinah
2014-02-09 17:27:30 cri
Gobarar da ta tashi a jiya ran 8 ga wata a wani otel dake Madinah, birni na biyu mafi girma a kasar Saudiyya, ta yi sanadiyyar mutuwar mahajjata 12, yayin da wasu fiye da 130 suka raunana.

Hukumomin birnin sun ba da sanarwa cewa, gobarar ta tashi a karfe 2 da mintoci 33 na yammacin ranar 8 ga wata a wani ginin dake gabashin birnin, wanda ya kunshe da mahajjatan fiye da 700 daga kasa da kasa. Bayan samun labarin, hukumar kwana-kwana ta tura motocin kashe wuta 18 zuwa wurin. Ban da haka, ma'aikatar kiwon lafiya ta tura motoci ba da jiyya cikin gaggawa 14 da rukunonin bada agaji 8 zuwa wuri domin ba da taimako.

Sanarwar ta ce, ma'aikatan kwana-kwana sun kwashe sa'o'i fiye da 2 suna kokarin kashe wutar. Yawancin mutanen sun mutu dalilin rashin iskar lunfashi, kana wadanda suka ji rauni an kai su asibitoci dake kewaye. Zuwa yanzu ana cigaba da bincike domin gano dalilin wannan gobara.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China