Kwamitin sulhu na M.D.D. ya bukaci Iran da ta tabbatar da tsaron hukumomi da jami'an diplomasiyya dake kasar
A ranar 4 ga wata, kwamitin sulhu na M.D.D. ya ba da wata sanarwa, inda ta yi kakkausar suka game da harin da aka kai ga ofishin jakadancin Saudiyya da ke kasar Iran, abun da ya kawo babban lahani ga yankin da kasashen suke ciki. Kwamitin sulhu na M.D.D. ya dora muhimmanci sosai game da wannan batu, inda ya bukaci gwamnatin Iran da ta sauke nauyin bisa kanta don tabbatar da tsaron hukumomin kasashen waje da ke kasar da jami'an diplomasiyya. A cikin sanarwar, an ce, kwamitin sulhu na M.D.D. ya bukaci bangarorin biyu da su yi shawarwari da daukar matakai don kawo sassauci ga halin kunci da ake ciki a wurin.
A wannan rana, zaunannen wakilin kasar Saudiyya a M.D.D. Abdullah Moalem ya fada wa kafofin yada labaru cewa, dauke dangantakar diplomasiyya tsakanin Saudiyya da Iran ba zai lahanta kokarin da Saudiyya ta yi game da yunkurin sassanta yanayin da ake ciki a Siriya da Yemen ba, Saudiyya tana da shirin shiga cikin shawarwari da za a yi tsakanin bangarorin daban daban na kasar Siriya a karshen wannan wata.(Bako)