Babban manajan kamfanin man fetur na kasar ta Iran Roknoddin Javadi ya bayyana cewa, ana fatan cinikin man fetur din zai kyautata dangantakar siyasa a tsakanin kasar Iran da kasar Masar. Ya kuma ce kasar Iran tana iya samar da albarkatun man fetur ga kasar Masar ba tare da gindaya wani sharadi ba, idan har gwamnatin kasar Masar ta bayyana bukatarta a hukunce, kasar Iran za ta yi la'akari da wannan batu ba tare da bata lokaci ba.
Tun a shekarar 1980 ne kasashen Iran da Masar suka yanke dangantakar diflomasiyya har ma da cinikayya a tsakaninsu tun bayan da kasashen Amurka da Turai suka kakabawa Iran takunkumi a shekarar 2012.
A 'yan watannin nan ne, bi da bi jami'an kasashen biyu suka bayyana fatan cewa, kawar da takunkumin da aka sanyawa kasar Iran, zai farfado da huldar ciniki tare da kyautata dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. (Maryam)