A wannan rana, a gun taron manema labaru, Joseph Biden ya bayyana cewa, sun san cewa zabi mafi kyau ne a kawar da barazanar kungiyar IS ta hanyar siyasa, amma kuma ba za a yi alkawarin rashin daukar matakan soja ba.
Ban da haka, Joseph Biden ya kara da cewa, kasashen biyu sun amince da karfafa hadin gwiwa a fannonin samun sakwannin asiri, da nuna goyon baya ga sojojin wurin da sauransu, domin yaki da kungiyar IS.
Kasar Turkiya ta yi iyaka da Syria da Iraki, shi ya sa ta masu tsattsauran ra'ayi su kan bi ta kasar domin shiga kungiyar IS. Sakamakon karuwar matsin lamba daga kasa da kasa, da abkuwar harin ta'addanci na kunar bakin wake da kungiyar IS ta yi, wanda a bara ya kai ga haddasa mutuwar mutane sama da 130 a birnin Ankara, hedkwatar kasar Turkiya, da yankin Sanliurfa dake kudu maso gabashin kasar, gwamnatin Turkiya ta kara karfin yaki da kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a kasar da dakaru masu tsattsauran ra'ayi dake ratsa kasar.(Fatima)