in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya fara ziyarar aiki a Iran
2016-01-23 12:31:00 cri
Jiya Jumma'a 22 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa babban birnin kasar Iran, Teheran, domin fara ziyarar aikinsa a wannan kasa dake yankin Gabas ta tsakiya, ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Javad Zarif ya tarbi shugaba Xi Jinping a filin jirgin sama da hannun biyu-biyu.

Xi Jinping ya mika sakon gaisuwa yayin saukar tasa da kuma nuna fatan alheri ga gwamnati da al'ummomin kasar Iran, haka kuma, ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Iran kasashe ne masu dogon tarihi a duniya, suna da tarihi da kuma al'adu dake cike da alfahari, sun kuma ba da babbar gudummawa ga ci gaban al'adun bil Adama a duniya. Kaza lika, tun da dadewa, al'ummomin kasashen biyu sun fara musayar al'adu da hajoji ta hanyar siliki, sa'an nan, bayan da aka kafa dangantakar diflomasiyyar dake tsakanin kasashen biyu, suna ci gaba da hakaba hadin gwiwar dake tsakanimsu a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu da dai sauransu.

A halin yanzu kuma, an gamu da wata sabuwar dama kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Iran, dalilin haka ne kasar Sin take fatan yin hadin gwiwa tare da kasar Iran domin kyautata dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da kuma hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa fannoni daban daban, ta yadda za a iya bude wani sabon shafi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Kaza lika, shugaban Xi Jinping ya nuna fatan yin shawarwari tare da shugabannin kasar Iran kan harkokin dake shafar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da wasu harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, domin tsara wani shirin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a iya karfafa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, yayin da ciyar da hadin gwiwar kasashen biyu gaba.

Shugaban Xi Jinping ya fara ziyarar aikinsa a kasar Iran bayan ya kammala ziyarar aiki a kasar Masar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China