Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei a birnin Tehran hedkwatar kasar a jiya Asabar 23 ga wata. Yayin ganawar tasu, Mista Xi ya ce, Sin da Iran sahihan abokai ne na aiwatar da tsarin "Ziri daya da Hanya daya", don haka Sin na fatan hadin gwiwa da Iran don tunbutar juna ta fuskar tsare-tsaren samun bunkasuwa, kuma za su kara hadin kai a wasu manyan fannoni bisa tsarin "Zirin daya da Hanya daya" ta yadda za su amfanawa jama'ar kasashen biyu da habaka zumunci tsakaninsu, ciki hadda manyan ababen more rayuwa, zirga-zirga, samar da kayayyaki da sauransu.
A nasa bangare, Ayatollah Ali Khamenei ya ce, Iran ta yaba matuka ga bunkasuwar da Sin take samu, kuma kasar na godiya sosai ga taimakon da Sin take ba ta a cikin dogon lokaci. Ayatollah Khamenei ya ce Iran na fatan tabbatar da dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare a dukan fannoni tare da kasar Sin, da ingiza hadin gwiwa tsakanin su zuwa wani sabon matsayi. Ya ce, tsarin "Ziri daya da Hanya daya" da Sin ta gabatar ya zo ne a daidai lokacin da ya dace, a matsayin muhimmiyar kasa wannan tsari ya shafa, Iran na fatan taka rawarta yadda ya kamata.
A wannan rana, shugaban Xi ya kuma gana da shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani. (Amina)