in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Iran
2016-01-24 13:05:43 cri

A jiya Asabar 23 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Iran, Hassan Rouhani a fadar Asadabad dake birnin Tehran.

A lokacin ganawar tasu bangarorin biyu suka waiwayi tarihin bunkasa dangantaka tsakanin kasashensu, da yin musayar ra'ayi kan hadin gwiwa tsakaninsu da sauran harkokin shiyya shiyya da na duniya da suka fi jawo hankula.

Shugabannin biyu sun kuma amince da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a dukkan fannoni, domin sa kaimi ga dangantakarsu zuwa wani sabon mataki, tare da kawo alheri ga jama'arsu.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin na fatan za a gudanar da yarjejeniyar batun nukiliya na Iran a dukkan fannoni lami lafiya, sannan ya yi marhabin da yadda Iran ta sake bayyana a dandalin shiyya shiyya da na duniya bisa wani sabon yanayi, da fatan kasashen biyu za su yi kokari tare, domin sa kaimi ga bunkasa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin siyasa, tattalin arziki, cinikayya, makamashi, manyan kayayyakin amfanin jama'a, tsaro da sauransu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, shugaba Hassan Rouhani ya furta cewa, shugaba Xi Jinping ya zama shugaban kasa na farko da ya kai ziyara a kasar Iran bayan warware batun nukiliya na kasar. Wannan ya nuna dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu.

Yace wannan ziyara za ta kasance isharar tarihin bunkasa dangantakar kasashen biyu kuma Iran tana dora muhimmanci kan muhimmiyar rawar da Sin take takawa cikin harkokin duniya, tare da nuna godiya ga taimako da goyon baya da kasar ta baiwa Iran. Haka kuma Shugaba Rouhani yace kasar sa ta yaba da gudummawar da Sin ta bayar wadda ta sa kaimi ga warware batun nukiliyar kasar ta hanyar siyasa.

Yace a wannan sabon yanayin da ake ciki, Iran na fatan ci gaba da yin mu'amala tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya.

Ya kara da cewa har ila yau kasar ta Iran tana son cigaba da hadin gwiwwa da Sin a fannin zuba jari, da makamashi, da hada hadar kudi, da kiyaye muhalli da dai sauransu, tare da shiga aikin raya "Ziri daya da hanya daya" cikin yakini, tare kuma da kara tuntubar juna kan harkokin duniya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China