Jam'iyyar CDU dake karkashin jagorancin Merkel ta kira wani taron koli a wannan rana, don tattauna kan laifin cin zarafin mata da sace-sace da suka faru a birnin Cologne dake yammacin kasar Jamus. Ya zuwa yanzu, al'amarin da ya faru a Cologne ya kara tsananta. Masu kyamar 'yan kasashen waje sun yi zanga-zanga a ran 9 ga wata a Cologne saboda ganin aukuwar al'amarin, zanga-zangat da suka yi ta haifar da rikici, abin da ya sa 'yan sandan wurin suka tarwatsa masu zanga-zanga da bindigar ruwa mai karfi tare kuma da cafke wasu daga cikinsu.
Taron koli kuma ya ba da sanarwar yin kira da a saukaka dokoki kan korar bakin da suka aikata laifi a kasar, idan wani dan gudun hijira ko wanda ya nemi samun mafaka sun aikata laifi kuma an yanke masa hukunci, ba zai sami iznin zama a Jamus ba, kuma za a kore shi. Bisa tanade-tanaden dokokin na yanzu a kasar ta Jamus, ba za a kori wanda yake neman mafaka daga kasar ba, sai dai idan ya aikata laifi da aka yanke masa hukunci da daurin shekaru 3 ko fiye a gidan kurkuku. (Amina)