in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu akwai jan aiki wajen tabbatar da dalilin faduwar jirgin saman Germanwings, a cewar shugaban Lufthansa
2015-04-02 10:52:46 cri
Jiya Laraba ranar 1 ga wata, yayin da babban jami'in zartaswa wato CEO na kamfanin jirgin saman Lufthansa,Carsten Spohr ke nuna jaje ga mutanen da suka rasu sakamakon hadarin jirgin sama mai samfurinA320 a yankin kudancin kasar Faransa, ya bayyana cewa, har yanzu akwai jan aiki wajen tabbatar da dalilin faduwar jirgin.

Bisa labarin da kafofin yada labarun kasar Faransa suka bayar, an ce, a wannan rana, Mr. Spohr da babban jami'in zartaswa na kamfanin jirgin saman Germanwings dake karkashin shugabancin kamfanin Lufthansa Thomas Winkelmann suka je kauyen Le Vernet dake dutsen Alps a kudancin kasar Faransa, don nuna juyayi ga dutsentunawa da wadanda suka mutu da aka kafa a wurin.

Spohr ya fada wa kafofin yada labaru cewa, " Ko wace rana, mun kara sanin wasu abubuwan dake shafar hadarin, amma har yanzu akwai jan aiki domin sanin ainihin abun da ya faru."

Amma yayin da aka tabo maganar rashin lafiya da mataimakin matukin jirgin saman Germanwings Andreas Lubitz yake da shi, Mr. Spohr bai ce kome ba game da batun.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China