Firaminitan kasar Sin Li Keqiang ya zanta da Merkel ta wayar tarho a daren ranar Litinin 23 ga wata, domin taya ta murna, inda ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana fatan kara habaka zumunci tsakaninta da Jamus. A nata bangare, Madam Merkel ta furta cewa, Jamus na fatan kara zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma kara habaka hadin kai a fannonin daban-daban.
Shugaban majalisar gudanarwa ta kungiyar kawancen kasashen Turai Mr Von Rompuy, da shugaban kasar Faransa Francois Hollande, su ma sun taya Merkel murnar lashe zaben. (Amina)