Bayan da aka kafa sabuwar gwamnatin Girka a karshen watan Janairun shekarar bana, ta bukaci Jamus sau da dama don ta biya kudin diyya na laifin yaki. A karshen watan Maris, yayin da firaministan kasar Alexis Tsipras ya ziyarci Jamus, ya gabatar da bukatarsa ga takwararsa ta Jamus Angela Merkel domin ganin Jamus ta biya wadannan kudade. A ranar 11 ga watan Maris, kakakin gwamnatin Jamus Steffen Seibert ya ce, ta fannin siyasa ko kuma ta fuskar doka, Jamus ta riga ta kammala biyan kudaden diyya da suka shafi yakin duniya na biyu. Ya ce, kullum Jamus ta kan tunawa da masifar da 'yan Nazi suka kawo wa kasashen Turai, kuma ta fahimta cewa, ya kamata Jamus ta dauki wannan alhakinta bisa tarihi, amma duk da haka, wannan ba zai canja ra'ayin gwamnatin Jamus ba, domin ta riga ta biya kudaden diyya ga kasashen da abin ya shafa a lokacin yakin duniya na biyu.(Bako)