in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Jamus ta gabatar da sakamakon babban zabe bisa mataki na farko
2013-09-23 16:37:59 cri

Bayan da aka kirga yawan kuri'un da aka samu daga dukan shiyyoyin zabe na kasar Jamus, gwamnatin kasar ta gabatar sakamakon farko a yau ranar 23 ga wata da sassafe cewa, jam'iyyar CDU/CSU dake karkashin jagorancin shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta samu kuri'u kashi 41.5 bisa dari wanda ya karu sosai bisa na adadin da ta samu a cikin zabe da aka yi a shekarar 2009.

Sakamakon kuwa ya nuna cewa, jam'iyyar GSDP ta samu kuri'u kashi 25.7 bisa dari wanda babu bambanci sosai bisa na zabe da ya gabata. Yawan kuri'un da Jam'iyyar FDP ta samu kuwa ya kai kashi 4.8 bisa dari wanda ya ragu matuka, kuma babu damar shiga sabuwar tarayyar majalisar dokoki. Jam'iyyar LPG da kuma ta DG fa, sun samu kuri'u na kashi 8.6 bisa dari da kashi 8.4 bisa dari. Sabuwar jam'iyyar da aka kafa a wannan shekara mai suna AG ta samu kuri'u na kashi 4.7 bisa dari kawai, wadda ita ma ba ta da damar shiga majalisar.

Duk da cewa, jami'iyyar CDU/CSU ta kai matsayi na farko a Tarayyar Jamus, amma ba ta samu kuri'u masu rinjaye ba, shi ya sa, ya kamata ta zabi wata jam'iyya ta daban domin tafiyar da mulkin kasar cikin hadin kai. Saboda jam'iyyar FDP wadda ta taba hada kai da Jam'iyyar CDU/CSU, amma yanzu ba ta da damar shiga majalisar, shi ya sa akwai bukatar Jam'iyyar CDU/CSU ta sake zabar abokiyarta don yin mulkin kasar ta hanyar hadin gwiwa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China