Kamfanin dillancin labaru na DPA na kasar Jamus ya ruwaito jami'in gwamnatin kasar na cewa, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ministocin da abin ya shafa sun tsaida wannnan kuduri ne a taron da aka gudanar a birnin Berlin a wannan rana. An bayyana cewa, gwamnatin kasar Jamus tana shirin tura jiragen saman bincike, wani jirgin ruwan yaki, jirgin saman samar da mai a yayin da jiragen yakin ke tafiya a sama a kalla daya, da kuma yin bincike ta tauraron dan Adam don nuna goyon baya ga Faransa.
A jiya shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana bayan da ya gana da shugaba Merkel a birnin Paris cewa, Faransa da Jamus za su hada kai don yaki da ta'addanci tare. Ministan harkokin tsaron kasar Jamus Ursula von der Leyen ya bayyana a jiya cewa, Jamus za ta kara tura sojoji zuwa kasar Mali don taimakawa kasar Faransa a kokarin da ta ke na tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali, hakan zai rage matsin lamba da kasar Faransa ke fuskanta a yakin da ta ke yi da kungiyar IS. (Zainab)