Robin ya ce, a yammacin wannan rana, wani sojin Faransa ya gano akwatin na biyu na jirgin a wurin da aka samu tarkaccen jirgin. Akwatin ya kone kwarai, amma duk da haka za a mika shi ga sashen bincike na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Faransa.
Jami'in ya kara da cewa, daga halin da ake ciki, ana fata zai kunshi wassu bayanai dake shafar jadawalin tafiye-tafiye don kara nazari. Har ila yau a wurin, an gano wayoyin salula 42 da suka lalace, wadanda ake ganin cewa, da kyar za a samu wasu bayanai masu amfani a ciki. Yanzu, masu binciken gawawwaki, sun samu bambancin kwayoyin halittar mutane wato DNA guda 150, kuma za a kwatanta su da dangogin wadanda suka mutu, amma ana bukatar karin makonni 3 zuwa 5 don gane gawawwakin mutane.(Bako)