Manyan jam'iyyu 5 na kasar ta Jamus ne dai aka sa ran za su fafata matuka a zaben. Kafin fara gudanar zaben, bisa binciken ra'ayoyin jama'a da aka yi, an ce, goyon bayan da bangarori biyu wato jam'iyyar dake kan karagar mulki da sauran jam'iyyun kasar suke samu ya yi kusa da juna. Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa za a kammala jefa kuri'un ne da karfe 6 na yammacin ranar ta yau bisa agogon wurin. Kuma gidan telebijin mallakar gwamnatin kasar zai bayyana sakamakon zaben da aka gudanar da maraice.
Don neman goyon baya na al'ummar kasar, shugabar gwamnatin kasar Jamus dake neman sake darewa mukaminta a karo na uku Angela Merkel ta yi wani jawabi a birnin Berlin a ranar Asabar 21 ga wata, inda ta ce, kiyaye darajar kudin Euro ya dace da moriyar kasar Jamus, kana zai iya tabbatar da inganta rayuwar jama'a da ayyukansu a kasar. Ban da wannan kuma, Merkel ta jaddada cewa, jam'iyyarta ta CDU/CSU ba za ta amincewa kungiyar EU ta gabatar da yarjejeniyar bashin hadin gwiwa ba, ta ce, matakan taimakon fita daga kangin bashi da kungiyar EU ke dauka kan kasashe masu bin bashi ba za su yi tasiri ga kasar Jamus ba. (Zainab)