Wasu jami'an 'yan sanda a kasar da suka shaida afkuwar lamarin sun ce, sama da mutane 70 ne suka mutu, sannan wasu sama da 100 suka jikkata sakamakon tashin boma bomai ba kakkautawa daga ranar Lahadin nan a shiyyar arewacin kasar.
Ministan Birtaniya mai kula da al'amurran Afrika James Duddridge, ya ce hare haren Boko Haram a kan fararen hula a 'yan kwanakin nan, a lokacin da suke ibada a masallatai ya nuna rashin imani da tausayi ga rayuwar bil adama.
Duddridge, ya ce Birtaniya ta yi Allah wadai da wadannan hare haren, sannan ta jajantawa iyalan wadanda hare haren ya rutsa da su.
Ministan ya ce Birtaniya za ta ci gaba da tallafawa Najeriya don yakar ta'addanci, sannan za ta samar da tallafi ga mutanen da rikicin na Boko Haram ya raba su da matsugunan su.
Hukumar 'yan sandan Najeriyar ta tabbatar da cewar, a ranar Litinin ne harin bom ya hallaka mutane masu yawa a wani masallaci a birnin Maiduguri, helkwatar jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.(Ahmad)