Kwamitin ya bayyana matukar damuwa game da karuwan kungoyoyin ta'addanci a yanzu da kuma nan gaba na kungiya mai tsattsauran ra'ayi da ake kira ISIL dake da alaka da Afghanistan.
Kwamitin ta kara wa'adin takunkumin wanda ya hada da daskarar da asusun ajiyar su, hana su tafiye tafiye,da kuma takunkumin makamai a kan daidaikun mutane da kungiyoyi.
Sai dai kuma , kwamitin ta lura da yadda yanayin tsaro da ake ciki a Afghanistan ya sassauta kuma wassu mambobin Taliban sun yi sulhu da gwamnatin kasar tare da goyon bayan a sulhunta tashin hankalin da ake cigaba da fuskanta a kasar ta hanyar lumana.
A don haka, kwamitin ta bayyana aniyar ta na cire takunkumin a kan wadanda suka yi sulhu.(Fatimah Jibril)