in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu ko jikkata ya karu zuwa 62 a Pakistan sakamakon girgizar kasa
2015-12-27 14:00:51 cri
A jiya Asabar 26 ga wata, kafofin yada labaru da jami'ai na Pakistan sun bayyana cewa, mutane biyu ne suka mutu yayin da wasu mutane 60 suka jikkata a Pakistan sakamakon abkuwar girgizar kasa mai karfin digiri 6.2 bisa ma'aunin Richter a arewa maso gabashin Afghanistan a daren ranar 25.

Hukumar kula da sufuri ta kasar Pakistan ta furta cewa, bala'in ya haddasa gangarowar duwatsu da laka a arewacin kasar, wadda ta hana zirga-zirgar a hanyar Karakoram. Yanzu ana kokarin kawar da duwatsu da laka domin sake amfani da hanyar.

Ban da haka, hukumar dake kula da bala'u ta kasar Pakistan tana kokarin yin bincike kan hakikanin yanayin da ake ciki bayan abkuwar bala'in, tare da yin gargadi ga al'ummar kasar da su mai da hankali kan sake yiyuwar wata girgizar kasa a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China