Bisa labarin da aka bayar, an ce, wassu 'yan ta'adda biyar ne suka kai hari kan wani otel inda sojojin kasar Amurka su kan yi masauki, wanda kuma ke kusa da ofishin jakadancin kasar Spaniya dake ta kasar Afghanistan. Haka kuma wassu masu dauke da makamai guda biyu sun kutsa cikin ofishin jakadancin kasar Spaniya, amma an harbe su biyu duka.
A wurin da aka samu fashewar, Mr. Mariano Rajoy, mataimakin ministan kula da harkokin cikin gidan kasar Afghanistan ya gaya wa manema labaru cewa, wannan hari ne na kunar bakin wake da wata kungiyar 'yan ta'adda ta shirya. Tuni dai kungiyar Taliban ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari. (Sanusi Chen)