Tuni dai kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin kara nanata matakan takunkumin da aka kakkabawa kungiyar Taliban da ma sauran kungiyoyin dake kawo barazana ga tsaron kasar Afghanistan, tare da jaddada cewa, kokarin dakatar dahanyoyin dake suke samun kudade da sauransu.
Wani jami'in bangaren 'yan sanda na kasar Afghanistan ya bayyana cewa, a jiya Litinin da karfe 9 na dare, dakaru sun harba makaman roka 3 a birnin Kabul, inda fadar shugaban kasar Afghanistan da hukumomin gwamnatin kasar da kuma wasu ofisoshin jakadanci na kasashen waje suke. Ya zuwa yanzu, gwamnatin Afghanistan ba ta bayyana adadin mutanen da suka mutu ko raunana ba.(Lami)