in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakin rigakafin ta'addanci na matsayin hudu a Brussels, in ji firaministan kasar
2015-11-23 10:47:26 cri

Faraministan Belgium Charles Michel ya sanar a ranar Lahadi da yamma a yayin wani taron manema labarai na ci gaba da ayyana matsayi na hudu na barazanar ta'addanci a birnin Brussels, kana bisa matsayi na uku a dukkan fadin kasar tun bayan wani sabon hasashen OCAM, wato hukumar dake daidaita da nazarin barazanar ta'addanci.

Ina tabbatar da cewa, muna fargabar wani hari ne irin na Paris, in ji mista Michel.

Faraministan ya sanar da wasu karin matakan tsaro bisa manyan matakai uku da suka hada da ci gaba da rike matakin karfafa yawan jami'an tsaro na 'yan sanda da sojoji a yankin Brussels, rage manyan bukukuwan dake janyo cinkoson jama'a, sannan mai da hankali musammmun ma ga harkokin sufurin jama'a da za su kasance rufe a ranar Litinin. Haka kuma, makarantu, jami'o'i za su kasance rufe a ranar Litinin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China