Gwamnan lardin na Helmand Mirza Khan Rahimi, shi ne ya tabbatarwa manema labarai aukuwar lamarin a jiya Alhamis. Rahimi ya ce sojojin gwamnati wadanda suka samu tallafi daga jiragen saman yaki, sun yi luguden wuta kan sansanonin 'yan Taliban a daren ranar Laraba.
A daya bangaren kuma, kwamandan sojojin gwamnatin kasar Abdul Manan Nijrabi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, an kaddamar da hare-haren na daren Laraba ne da taimakon dakarun kungiyar tsaro ta NATO ko RS a takaice, lamarin da a cewar sa ya haddasa kisan mayakan Taliban da jikkatar wasu sama da 100.
Kawo yanzu dai kungiyar ta Taliban ba ta ce komai game da aukuwar lamarin ba. Gabanin kaddamar da farmakin, mayakan Taliban sun datse hanyar dake bi domin kai kayayyaki ga sojojin gwamnatin dake Lashkar Gah, hedkwatar lardin Helmand dake kudancin kasar.(Saminu Alhassan)