A cikin wata bukatar da aka amince da ita a wannan ranar, kasashe 15 mambobin kwamitin sun ce sun yi shawarar kara adadin sojin na ofishin zuwa kusan 13,000 sannnan su kara 'yan sanda 2,001 da suka hada da 'yan sanda masu zaman kansu, da 'yan sanda masu kwantar da tarzoma, gami da jami'an gidan yari 78.
Ofishin zai kuma dauki nauyin taimaka ma ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da jami'iyyun siyasa masu ruwa da tsaki a kasar suka rattaba ma hannu. Haka kuma an dora ma ofishin nauyin kare rayukan fararen hula da samar da taimakon jin kai.
Har ila yau a ranar tarlatan kwamitin ya yi shawarar kara wa'adin ayyukan ofishin zaman lafiya a yankin Abyei wato UNISFA zuwa ranar 15 ga Mayun badi.
Abyei dai yankin ne da ake takaddama a kai tsakanin kasashen biyu wato Sudan da Sudan ta kudu. Kwamitin sulhun Majalissar ta kirkiro da ofishin a shawarar da ta zarata a ranar 27 ga Yunin shekara ta 2011 sakamakon damuwar da take da shi game da tashin hankalin, ruruwar wutar rikici da kuma raba jama'a da muhallan su a cikin makonni kafin a ba kasar ta Sudan ta kudu 'yancin kai. (Fatimah Jibril)