in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun yi magana ta wayar tarho
2015-12-11 16:51:34 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bugawa takwaransa na kasar Amurka Barack Obama wayar tarho a ran Jumma'an nan 11 ga wata, inda ya nuna cewa, ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu bai daya.

Shugaba Xi ya ce a don haka yana fatan Amurka ta nuna niyyar hadin gwiwa da Sin don warware tare da magance wasu bambancin ra'ayi da batutuwa da suka fi jawo hankalinsu, ta yadda za a raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.

Ban da wannan kuma, Mista Xi ya jaddada cewa, an kusan kamala taron sauyin yanayi na birnin Paris, don haka Sin da Amurka dukkansu na neman bangarori daban-daban dake halartar taron da su kara mu'ammala da hadin gwiwa don ba da tabbaci ga a kai ga wata yarjejeniya, matakin da zai amfanawa kasashen duniya.A nashi bangare, Mista Obama ya ce, ya yi farin ciki sosai da ganawa da Mista Xi a taron sauyin yanayi da aka yi a birnin Paris, inda bangarorin daban-daban suka tattauna tare da sulhunta tsakaninsu. Ya ce Amurka za ta ci gaba da mu'ammala da kasar Sin don hazarta a samun sakamako mai kyau a taron.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China