A yau ne shugaba kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taro na 19 game da zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje daga dukkan fannoni .
A jawabinsa yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, daga farkon wannan shekara, kasar Sin ta aiwatar da wasu manufofi na yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, a kokarin raya sassa daban-daban na kasar yadda ya kamata.
Shekara mai zuwa, shekara ce da aka fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13. Don haka dole ne a mai da hankali kan raya zaman al'umma mai wadata da kuma bullo da sabbin matakan raya kasa, yayin da ake aiwatar da manufofin, da kyautata tsare-tsare, a kokarin aiwatar da manufofin da aka tsara. (Tasallah Yuan)