A ganawar da ya yi da Firaministan kasar ta Masar Sherif Ismaila a ranar jumma'an nan a gyefen wajen taron FOCAC a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu, Shugaba shugaba Xi ya ce ya kamata a bunkasa manyan ayyukan samar da kayayyaki a bangaren lantarki, sufuri da gina ababen more rayuwa a karkashin shirin ziri daya hanya daya.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan shirin kasar Masar na samar da zaman lafiya da cigaba kuma a shirye take ta hada kai da kasar Masar don daga matsayin hadin gwiwwar dake tsakaninbangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare gaba..
A nasa bangaren, Firaministan firaministan kasar Masar Sherif Ismail ya yaba matuka da jawabin da Shugaba shugaba Xi Jinping ya gabatar a bikin bude taron na FOCAC, inda ya ce jawabin zai kara haifar da sakamako mai kyau kan gwiwa tsakanin Sin da Afrika.