Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron tsaron yanar gizo na kasa da kasa da za a gudana daga ranar 16 zuwa 18 ga wata a garin Wuzhen na lardin Zhejiang.
Direktan ofishin kula da yanar gizo ta Intanet na kasar Sin Mista Lu Wei shi ne ya sanar da hakan a taron manema labaran da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira a yau Laraba.
Rahotanni na cewa, an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba game da taron na wannan karo da ake ganin ya dara wanda aka yi a shekarar bara.
Ana sa ran wakilai fiye da 2000, ciki har da shugabannin kasashen waje 8, manyan jami'ai kimanin 50 daga kasashe ko yankuna fiye da 120 daga nahiyoyi biyar ne za su halarci taron, inda ake sa ran tattauna abubuwan da suka shafi fannonin Intanet daban-daban. (Amina)