Mr. Shen ya ce sabbin matakan za su kunshi abubuwa iri iri, wadanda za su bayyana sabbin alamun hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, da biyan bukatunsu a fannin tsarin bunkasuwa, da hadin gwiwa tsakaninsu, tare da samun fasahohi da nasarori tare.
Game da jita jitar da wasu suke yadawa a Afirka, cewa wai Sin na barazana ga nahiyar, kuma abin da take yi a Afirka mulkin mallaka ne na sabon salo, da kuma tababar da ake yi game da manufar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, Mr. Shen Danyang ya bayyana cewa, ana nuna tababar ne ba tare da la'akari da hakikanin abubuwan dake abkuwa ba, ba kuma tare da duba hakikanin yanayin da ake ciki a fannin dangantakar Sin da kasashen na Afirka ba. Ya ce tun asali, kasar Sin aminiyar nahiyar Afirka ce, hakan kuma zai ci gaba da dorewa nan gaba da ma ko da yaushe. (Fatima)