Shugaba Xi ya ce, namun daji muhimmin kashi ne na halittu, wadanda suke da alaka matuka da dauwamammen ci gaba na bil'adama.
Baya ga haka, shugaba Xi ya jaddada cewa Sin tana dora muhimmanci sosai ga aikin kare namun daji, kuma ta kara karfin kiyaye wuraren da namun daji ke rayuwa da haihuwarsu, da yaki da fasa kwaurin sassan jikin namun daji, kamar hauren gwiwa da sauransu, aikin da kuma ya samu gagarumar nasara.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kare rayuwar namun daji, wani muhimmin kashi ne na hadin gwiwa tsakanin Sin da Zimbabwe. Kaza lika Sin za ta ci gaba da taimakawa Zimbabwe a wannan fanni, ta hanyar ba da kyautar kayayyaki da fasahohi domin ci gaba da cimma nasarar hakan. (Fatima)