Dandalin sauyin yanayi da ci gaba a nahiyar Afrika karo na biyar da ake yi, musammun ma domin tattauna amsar da Afrika za ta bullo da ita kan sauyin yanayi, ya bude a ranar Laraba a yankin bakin ruwa na Victoria Falls dake kasar Zimbabwe.
Dandalin na kwanaki uku na da manufar baiwa kasashen Afrika damar shirya taron sauyin yanayi na majalisar dinkin duniya da zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa daga bakin ranar 30 ga watan Nuwamba.
Mataimakin shugaban kasar Zambabwe, Emmerson Mnangagwa ya bude taron a gaban wakilai fiye da 400, tare da yin kira ga kasashen Afrika da su hada kansu, da cimma wata matsaya guda kan sauyin yanayi.
Taron Paris zai samar da wata sabuwar yarjejeniya kan yanayi wacce za ta shimfida harsashe na gari kan yanayin duniya na lokacin bayan yarjejeniyar Kyoto.
Haka kuma, taron Paris zai gudana a lokacin da Afrika, da ma sauran kasashe masu tasowa suke fuskantar matsalar sauyin yanayi dalilin tasirin da bai taka kara ya karya ba wajen aiwatar da karfin rage kaifin sauyin yanayi.
Nahiyar Afrika na fatan kudaden da za a zuba kan batun sauyin yanayi, za a rarraba su bisa daidai bukatun ko wane bangare tsakanin dabarun aiwatarwa da kuma rage kaifin matsalar, ta yadda nahiyar Afrika za ta samu zarafin fuskantar sauyin yanayi da kai ga ci gaba mai dorewa, in ji madam Fatima Denton, darektar sashen dabarun musammun na kwamitin tattalin arziki na MDD reshen Afrika. (Maman Ada)