A gun taron manema labaru da ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan kasar ta shirya, ministan ya bayyana cewa 'yan sanda kimanin 8000 ne za su gudanar da bincike a kan iyakokin kasar ta Faransa. A sa'i daya kuma, za a kara tura ma'aikata kimanin 2800 don tabbatar da tsaron a wurin taron.
Har wa yau a daya bangaren, rundunar sojin birnin na Paris ta ce domin saukakawa shugabannin kasashen duniya zirga-zirga, da isa wurin da za a gudanar da taron, za a dauki matakan hana zirga-zirgar motoci a wasu hanyoyi da ke kewayen birnin Paris, da ma wasu manyan hanyoyi, baya ga hanyoyin da ke kewayen manyan filayen jiragen sama na Charles de Gaulle, da na Orly dake birnin.
Fadar shugaban kasar Faransa ta bayyana cewa, an gayyaci shugabanni da kusoshin gwamnatocin kasashe 138 don halartar taron.(Bako)