Hollande ya ce, harin da aka kai birnin Paris a daren ranar 13 ga wata, ya haddasa mutuwar mutane a kalla 129, kuma Hollande ya mayar da lamarin a matsayin yaki. Don haka ya yi kira ga kasashen kungiyar EU da su inganta hadin gwiwa don yaki da ta'addanci, da amfani da bayanan da suka samu kan yaki da fasa kwaurin makamai, da binciken iyakokin kasar, da cafke 'yan ta'adda. Hollande ya ce, za a gabatarwa majalisar dokokin kasar wani shirin daftari, don tsawaita dokar ta baci da aka sanya a kasar na tsawon watanni 3. Ya kuma bukaci firaministan Faransa da ya gabatar da shirin yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, da yin kwaskwarima game da dokar da ta baiwa jama'a damar rike takardun fasfot guda 2, da asalinsu. Ya kuma sanar da cewa, za a inganta matakan tsaro a kasar Faransa, don samar da guraben aikin yi 5000 cikin shekaru 2 masu zuwa, kuma za a inganta harkokin sojin kasar.
A wannan rana, mataimakin ministan harkokin waje mai kula da harkokin yaki da ta'addanci na Rasha Oleg Syromolotov ya ce, ya kamata bangarorin da abun ya shafa su kulla wani kawance bisa dokoki a kokarin da ake na yaki da IS, ya kamata a martaba dokokin kasa da kasa da girmama 'yancin kasa a yayin wannan kawacen karkashin shugabancin M.D.D.. Ya jaddada cewa, Rasha za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kwamitin yaki da ta'addanci na kwamitin sulhu na M.D.D. Ya kuma bayyana cewa, IS tana barazana ga yankunan tsakiyar Asiya, kuma wannan yana haifar da babbar barazanar tsaro ga kasar Rasha.(Bako)