Ministan noma, albarkatun ruwa da tsaron abinci na kasar Burkina Faso ya kaddamar a birnin Manga dake tsakiya maso kudancin kasar da wani shirin da aka ma taken "Shiri na daya na tsarin karfafa karfin tsaron abinci da abinci mai gina jiki a yankin Sahel".
Bisa jimillar kudin Sefa biliyan 22,700, wannan shiri zai shafi gundumomi 92 da aka rarraba su zuwa yankuna 6, da suka hada da mahadar Mouhoun, tsakiya maso yammaci, tudun tsakiya, tsakiya, Sahel da tsakiya maso kudanci, in ji wata sanarwa ta cibiyar watsa labarai ta gwamnatin kasar (SIG). (Maman Ada)