in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan Faransa game da yaki da ta'addanci, in ji ma'aikatar harkokin waje
2015-11-16 19:36:43 cri
A yau Litinin 16 ga watan nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei, ya bayyanawa taron manema labaru da aka shirya a birnin Beijing cewa, ta'addanci ya kasance babban kalubale ga bil'adam baki daya, shi ya sa kasar Sin ke nuna goyon baya ga kasar Faransa wajen yaki da shi.

Mista Hong ya ce, ta'addanci ya kasance babban kalubale ga bil'adam baki daya, kuma kasar Sin ita ma ta sha wahalhalu da dama wadanda suka shafi hakan, shi ya sa take kokarin shiga ayyukan yaki da ta'addanci na kasashen duniya cikin yakini.

Ya ce Sin na kyamar kowane irin nau'in aikin ta'addanci, kuma tana nuna goyon baya ga kasar Faransa wajen yaki da shi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Bugu da kari kasar Sin tana ganin cewa, kamata ya yi kasashen duniya su hada kansu domin kawar da ta'addanci daga tushensa. Dadin dadawa, ya dace MDD ta taka rawar a zo a gani wajen hada kan kasa da kasa ta fannin yaki da ta'addanci.

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, kungiyar "East Turkestan Islamic Movement" ko (ETIM) a takaice, da ma sauran kungiyoyin ta'addanci, baya ga kasar Sin, irin wadannan kungiyoyi na kawo barazana a sauran kasashen duniya baki daya. A sabili da haka, kamata ya yi a dauki aikin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a matsayin wani muhimmin bangare na aikin yaki da ta'addanci a duniya baki daya. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China