Shugaban Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa, kamata ya yi yarjejeniyar sauyin yanayi da za a cimma a nan gaba ta kare 'yancin kasashe masu tasowa.
Shugaban ya kara da cewa, kamata ya yi kasashe masu tasowa su samu tallafin da suke bukata, ta yadda za su iya rage fitar da iskar da ke dumama yanayin duniya zuwa yanayin duniyar da ba ya gurbata muhalli.
Shugaba Zuba yana bayyana matsayin kasarsa ce game da taron canjin yanayi gabanin taron kalin canjin yanayi na MDD da za a gudanar a birnin Paris na kasar Faransa a karshen watan Nuwamba zuwa tsakiyar watan Disamban wannan shekara.
Zuma ya ce, taron na birnin Paris wata dama ce ga kasashen duniya su hada kai wajen bullo da matakan tunkarar matsalar canjin yanayin duniya, sannan su gaggauta bullo da wata yarjejeniya a hukumance da za ta tilastawa dukkan kasashe daukar matakai magance matsalar canjin yanayi.
A matsayinsa na shugaban kungiyar G77 da kasar Sin, kana mamba a kungiyar masu shiga tsakani na Afirka (AGN) da Brazil da Afirka ta Kudu da Indiya da Sin (BACIS), Zuma ya bayyana cewa, kasarsa tana da nauyi na musamman na gabatar da muradun kasashe masu tasowa a taron na Paris.(Ibrahim)