Ya ce hakika faretin ya kayatar, ya kuma bayyana karfin kasar ta Sin a fannin aikin soji, da kuma niyyarta ta ci gaba da amfani da ikon da take da shi wajen wanzar da tsaro, da zaman lafiya da lumana a duniya baki daya.
Zuma ya ce kasarsa, ta yi matukar farin cikin gayyatar da ta samu na halartar wannan biki na bana, musamman kasancewar Sin kasar dake goyon bayan manufar kyamar nuna karfin tuwo, da tsaron yankunanta, da kuma bunkasa manufar watsi da amfani da karfi a duniya baki daya.
Bugu da kari shugaban na Afirka ta Kudu, ya jaddada muhimmnacin rawar da Sin ta taka wajen goyon bayan manufar samun 'yancin kan kasashen Afirka. Hakan a cewarsa ya dada fitowa fili, idan aka dubi yadda kasashen na Afirka 9 suka halarci bikin na bana.
Daga nan sai ya bayyana muhimmnacin koyi daga Sin, yana mai cewa kishin kasa da da'a, na cikin muhimman darussa da nahiyar Afirka ka iya koya daga Sin. Ya kuma yi fatan ganin kasarsa ta karfafa ikonta a fannin tsaro, ta yadda hakan zai zamo daya daga cikin matakai na wanzar da tsaro, da zaman lafiya a nahiyar Afirka baki daya. (Saminu Hassan)