in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi: kasar Sin tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasuwar tattalin arzikin duniya da na Afirka
2015-10-10 18:15:33 cri
Mamba a majalisar gudanarwa ta kasar Sin Yang Jiechi wanda yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar Afirka ta kudu ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kashi 7% a farkon rabin wannan shekara, abin da ya sanya kasar kan gaba a kasashen duniya ta fannin bunkasuwar tattalin arziki, kuma irin halin da ake ciki ba zai canza ba cikin wani dogon lokaci. A farkon rabin wannan shekara, kashi 30% na bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta danganta ne ga kasar Sin, kuma kasar ta taka rawar gani a wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin Afirka. Alkaluman kididdiga sun shaida cewa, kasar Sin ta ci gaba da ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya da kuma na Afirka.(Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China