Mista Yang ya bayyana cewa, ziyararsa a wannan karo na da zummar yin musayar ra'ayi kan yadda za a shirya wannan taro da za a yi a watan Disamba na bana a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu. A cewarsa, tun kafuwar wannan dandali na tsawon shekaru 15 da suka gabata, bangarorin biyu na samun ci gaba mai armashi a fannoni daban-daban cikin hadin gwiwa.
Ban da wannan kuma, Mista Yang ya ce, yanzu dandalin ya zama wani tsari mai inganci wajen yin musayar ra'ayi da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika.
Dadin dadawa, Mista Yang ya kara da cewa, Sin na fatan nacewa ga manufar zaman daidaici da shawarwari da juna, don gudanar da taron tare da kasashe 50 na Afirka, ta yadda za a mai da taron wani gaggarumin biki ne dake kara hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da kuma habaka dangantakar dake tsakaninsu nan gaba. (Amina)